An Baiwa Gwamnatin Kano Shawarar Dakatar Da Sarki Sanusi Lamido Sanusi

A cikin binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ke yi na zargin almubazziranci da kudaden majalisar masarautar Kano, Hukumar ta shawarci gwamnatin jihar da ta dakatar da sarki Sanusi Lamido Sanusi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta shawarci gwamnatin jihar ta dakatar da mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi, tare da wasu ma'aikatan sa su uku domin bata sukunin ci gaba da binciken da take game da zargin almubazziranci da kudaden majalisar masarautar ta Kano kimanin naira biliyan uku.

A cewar shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, sun bada shawarar dakatar da sarkin ne bisa dalilai da yawa wanda suka hada da ana so ayi amfani da damar masarautar ne domin a makure binciken da suke gudanarwa, don haka ne suka bayar da shawarci dakatar da Sarkin da duk wanda suke da hannun ciki.

Ya kara da cewa sun gano bayanai kudade da dama daga kamfanoni da bankuna wanda aka kashe ba bisa ka’ida ba.

Hakan na kunshe ne cikin sakamakon farko na binciken da hukumar ta fara tun a shekara ta 2017 wadda hukumar ta mika ofishin sakataren gwamnatin jihar.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari Dauke Da Cikakken Rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

An Baiwa Gwamnatin Kano Shawarar Dakatar Da Sarki Sanusi Lamido Sanusi