An ba Yara Miliyan 3 da Dubu 400 Maganin Polio a Jihar Kaduna

Wasu nakasassu a Kano.

Wani jami’in hukumar kiwon lafiya matakin farko ta Jihar yace an yi ma yaran rigakafi ne a zagaye na baya-bayan nan da aka kamala ranar 17 ga wata.
Wani jami’in hukumar kiwon lafiya matakin farko ta Jihar yace an yi ma yaran rigakafi ne a zagaye na baya-bayan nan da aka kamala ranar 17 ga wata.

An ba yara su miliyan 3 da dubu 400 maganin rigakafin cutar shan inna ko Polio a Jihar Kaduna, a zagaye na baya-bayan nan na kyamfe din yaki da cutar da aka kamala ranar 17 ga watan nan na Disamba.

Wani jami’in hukumar kiwon lafiya matakin farko a jihar Kaduna, Alhaji Hamza Ikara, yace wannan adadin kimanin kasha 80 cikin 100 ne na yawan yaran da aka so ba su wannan maganin rigakafi.

Yace an samu nasarar gudanar da wannan aiki a dukkan yankunan kananan hukumomi 23 na jihar, kuma nan da ‘yan shekaru kadan za a ga bayan wannan cuta a duk jihar.

Jami’in yace yanzu watanni 12 ke nan ba a samu bullar cutar Polio a jihar ba, yana mai cewa rashin yarda daga bangaren wasu iyayen yara shi ne ya sa ba a samu cimma kasha 100 bisa 100 na karbar maganin ba.

Ya yaba da irin rawar ganin da kungiyoyin mata da na matasa, da kungiyoyin addini tare da sarakunan gargajiya suka taka wajen cimma nasarar wannan shirin.