Kungiyoyi da ke rajin kare rayuwar matasa da tare da hadin gwiwar hukumar matasan da ke yi wa kasa hidima, sun yi kira ga matasa da su dukufa wajen nemarwa kansu sana’oi ba tare da sun dogara da ayyukan gwamnatin ba.
An yi wannan kira ne yayin da aka yi bikin ranar tunawa da matasa a karshen makon da ya gabata, wanda ya gudana a Jami’ar Bayero da ke Kano, domin bin sahun sauran kasashen duniya da ke bikin wannan rana ta matasa.
Taron na wannan shekara ya fi mai da hankali ne kan irin rawar da matasa ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’uma.
“Sakon da muka zo mu su da shi na yau shi ne su farga su daina jira cewa dole sai sun sami aikin gwamnati, saboda idan ka duba, guraban da ake da su a ma’aikatun gwamnati ba za su iya daukan dukkan matasan da muke da su a Najeriya ba.” In Ji Malama Hauwa Liman, Darekta a kungiyar wayar da kan matasa ta Impact Nigeria Project.
Farfesa Habu Muhammad Fagge, na daga cikin kwararru da suka gabatar da mukaloli a gaban wannan taro, ya kuma yi kira ga matasan da su guji zama masu ta da husuma.
“Matasa na yanzu, wadanda su ake kira manyan gobe, ya kamata su ce a’a, ba mu yadda da wani ta bayan fage ya zo ya ce mana wai mu tashi mu yi rikicin raba kasar nan ba, ko kuma a’a bari mu tashi mu yi rikicin siyasa domin a cimma burin mutum daya.”
Saurari cikakken rahoton wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari domin jin cikakken bayani kan wannan rahoto:
Your browser doesn’t support HTML5