An Azabtar Da Wasu Yara Mata Har Daya Ta Mutu

Rundunar ‘yan Sandan jihar Gombe, ta cafke wasu mutane ukku, da ake zargin da hadin baki domin azabtar da wasu matasan mata su biyu, wadanda ake wai zargi da maita.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan na jihar Gombe, Ahmed Usman, ya ce yaran masu shekaru goma sha ukku da shekaru tara, su kwashe mako biyu ana gana masu azaba, ne domin wai an zargi cewa suna da maita wanda daga bisani Abigail Lara, mai shekaru tara ta mutu.

Ya kara da cewa baya duka da dorina da aka yi masu an kuma yi amfani da sukundireba, wajan azabatar da yaran wanda ya barsu da miki a jiki.

Wadanda ake zargin da azabtar da yaran James Awak,Adamu Zakka da Hannatu Awak, tuni aka gurfanar dasu a gaban kuliya a cewar kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar.