An Alakanta Yawan Shan Kwayoyi A Borno Da Yakin Boko Haram

Wasu daga cikin irin kwayoyin da ake yawan sha a yammacin duniya.

Likitan kwakwalwa kuma babban Jami’i a asibitin masu tabin hankali na Maiduguri, Jahar Borno, Dr Ibrahim Abdullahi Wakawa, ya tattauna da Muryar Amurka akan ranar yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi da majalissar dinkin duniya ta ware domin tunatar da duniya kan illolin da ta’ammali da miyagun kwayoyi ke haddasawa.

Dr Ibrahim Abdullahi ya ce a shekarar da ta gabata a Najeriya an gudanar da wani binciken da ya nuna cewa kashi goma sha hudu cikin dari na al’umar Najeriya su na ta’ammali da miyagun kwayoyi da yake gusher da hankali mutane wanda hakan na nufin daya daga cikin mutane shidda za’a iya samun mai amfani da kwaya.

A Jahar Borno kuma binciken ya nuna kusan kashi tara cikin dari wato kowane mutum daya cikin goma na amfani da miyagun kwayoyi, hakan ya sake muni ne sanadiyar wannan rikicin da aka samu a wannan yankin, ya sa mutane da yawa sun samu kawunansu cikin mawuyacin rayuwa da ya ta’azzara su suke amfani da miyagun kwayoyi, idan aka duba shekarun da suka gabata da wuya kaga mata na ta’ammali da miyagun kwayoyi amma yanzu za ka ga mata na shaye-shayen miyagun kwayoyi, Inda bincken ya nuna cewa mata kashi shida cikin dari suna shan miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa binciken ya nuna cewa matasa masu shekaru goma sha biyar zuwa hamsin ne, su ka fi ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Ga Haruna Dauda Biu Dauke Da Rahoton Cikin Sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumomi Sun Alakanta Yawan Amfani Da Miyagun Kwayoyi A Borno Da Yakin Boko Haram