An Alakanta Rikicin Falasdinawa da Yahudawa Da Kyamar Jinsi

  • Ibrahim Garba

Al- Aksa, Birnin Kudus

Wasu malamai sun lura cewa rikicin Falasdinu na da nasaba da wariyar jinsi. Don haka sun ce sai an shawo kan wannan matsala ta sauya tunanin mututanen yankin ga tafarkin zama tare kafin a yi nasarar tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Kungiyar ‘Yan’uwa Musulmi a Najeriya ta shirya wani babban taron tunawa da Birnin Kudus; Qudus Day, a Turance, inda wani malamin addinin Musulunci mai suna Imam Muhammad Al’asi daga birnin Washington na Amurka ya ce alakanta takaddamar Falasdinawa da Isira’ilawa da wariyar jinsi da kuma yadda ake fassara Attaurah da Injila. Ya ce irin wannan fassarar na nuna cewa Falasdinawa ba su cancanci zama a Falasdinu, don haka, in ji shi, Falasdinawa kimanin miliyan 45 ne su ka bar Falasdinun kuma ba su da sukunin dawowa.

Ya ce don haka ba kawai wajibi ne a kwato ma Falasdinawa ‘yancin su ba, ya kuma kamata a sauya tunanin Yahudawa masu ganin su wasu mutane ne na musamman.

Shi kuwa Shugaban kungiyar ta ‘Yan’uwa Musulmi a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky cewa ya yi samar da ‘yanci ga Falasdinawa aiki ne da ya shafi kowa. Y ace ba kawai aiki ne na Musulmi ko na ‘yan Shi’a kawai ba, a’a na daukacin dan’adam ne.

Shi kuwa wani Rabaran da ya halarci taron daga Kaduna mai suna Yohanna Y.D. Buru, y ace tashin hankalin Gabas Ta Tsakiya wani hukuncin Ubangiji ne ga Yahudawa saboda saba ma Allah da su ka yi tun zamanin Annabi Musa. Ya kawo Alkalawa 2:3-5. Y ace ‘yan Shi’a na daukar maganar Birnin Qudus da karfi kamar yadda su ma Yahudawa su ke daukawa. To amma y ace tashin hankalin da ISIS ke yi a yanzu wasan yara ne ma kawai - ya ce idan Mahdi ya bayyana ne za a san gaskiyar al’amarin - ya ce ko Amurka da da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Larabawa ba za su iya warware matsalar ba. Nasiru Adamu Elhikaya ya aiko da rahoton daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bayyana Rikicin Isira’ila da Yahudawa Da Kyamar Jinsi - 2'57''