A Jamhuriyar Nijar, jam’iyyun kawancen hamayya sun gudanar da jerin
gwano hade da taron gangami a yau lahdi a birnin Yamai domin
kalubalantar gwamnatin Mahammadu Isuhu da suke zargi da niyyar
tafka magudi a zabubukan da za a yi badi a Nijar.
Wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma ya aiko mana da wannan rahoton.
Zargin gwamnatin Jamhuriya ta bakwai da kokarin shirya magudi a
zabubukan badi hade da nuna kin yarda da sahihancin kotun tasrin
mulkin kasa, sune manyan batutuwan da suka kai kawancen ‘yan
hamayya fitowa titunan Yamai domin jan hankalin mahukuntan kasar
Nijar su canza tunani kamar yadda Madame Bayer Maryama
Gamatche ke fada a gaban dubban magoya bayan FPR da suka yi jerin
gwano daga dandalin Place Toumo zuwa dandalin Place de la
Concertation.
To sai dai a nasu bangare, shugabannin jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulki,
a ta bakin Alhaji Asumana Mahammadu, sun musanta wannan zargi.
Wannan shine karon farko da ‘yan adawa ke fitowa kan tituna, tun
bayan zanga zangar da suka gudanar a farkon wannan shekara ta 2015
inda aka yi ba ta kashi tsakaninsu da jami’an tsaro saboda dalilan da
hukumomin Yamai suka kira na rashin bayar da izini.
Your browser doesn’t support HTML5