Ganin cewa zabubbuka a Najeriya, ya tunkaru wani babban batu dake ci gaba da daukar hankalin jama’a, a yanzu kuma mai bada fargaba shine, yadda makamai, ke ci gaba da bazuwa, a hannun jama’a, kuma ba bisa ka’ida ba.
Wannan lamarin ba zai haifar da dan mai ido ba masamman ma idan aka yi la’akari da yadda hanyoyin ruwa jihar Rivers suke dake yankin Niger Delta, da kuma yadda ake tunanin zabubbukan zasu gudana a cikin nasara.
Kawo yanzu dai akwai bayanai da suka tabbatar da cewa lallai akwai makamai dake ci gaba da bazuwa hannayen jama’a, a jihar ta Rivers.
Yayi da rundunar ‘yan Sandan jihar, tace ta na samun nasarar kau dasu daga hanu jama’a, DSP, Ahmed Kidaya Muhammad, mai Magana da yawun rundunar ‘yan Sandan jihar Rivers, yace “Mun kama makamai da dama a hannayen da bai kamata bam un fitar da wata sanarwa inda muka bukaci wadanda muka baiwa lasisin mallakar bindiga, toh wannan lasisin an dakatar dashi su dauki duk makaman da suke dashi su kai ofishin ‘yan Sanda mafi kusa dasu, kuma duk wanda aka kama da makami zamu tuhumeshi a matsayin mai aikata muggan laifuffuka.”
Your browser doesn’t support HTML5