Yayin da gwamnatin kasar zata tsaya taga irin rawar da Shugaba Donald Trump zai taka wanda ko zai dauki mataki mai tsauri akan wannan shugaban ko kuma a’a.
A ranar Talata ce dai Kungiyar ta ‘yan ba ruwan mu da ba wani yawa ke garesu ba a majilisar wakilan, wadanda suka hada da ‘yan jamiyyun biyu, wato Democrat da Republican suka shaidawa kungiyar Iraniyawa ‘yan Amurka hakan.
Kungiyar taIraniyawa dake nan Amurka ta kira ‘yan majilisar yayin wani taro nasu domin ‘yan majilsar su gabatar da jawabi sai dai kuma wannan wani yunkuri ne daga kungiyar ta ‘yan Iran na ganin sunyi kamun kafa ga ‘yan majilisar dokokin akan batun kungiyar wadda ake mata kalon babbar ‘yar adawa.
Kungiyar tace tana kira da a samar da gwamnatin demokaradiyya gwamnatin da bata da alaka da makamin nukiliya a kasar tasu ta Iran.
Ita dai wannan kungiyar ita ce ta jagoranci wata kungiyar yan adawa na kasar Iran dake da mazauni a kasar Faransa data yi kokarin ganin an ture gwamnatin kama karya ta kasar Iran din.
A cikin jawabin sa wajen taron babban darektan kungiyar Majid Sadeghpour yace yana fata ganin kungiyar tayi aiki da gwamnatin Donald Trump da ma majilisar dokokin Amurka domin samar da manufofi nagartattu akan kasar ta Iran.