Amurkawa Na Bikin Ranar Cika-Ciki

Shugaban Amurka Joe Biden yanawa Amurkawa barka da ranar cika ciki wato Thanksgiving - Ga tolotolon da za su yanka

Wannan ranar ta hutu ce a fadin Amurka inda Amurkawa na shakatawa tare da cin abinci da gudanar da tarukan tuntubar juna da zuwa kantuna tare da iyali domin sayen kayan marmari.

Alhamis 28 ga watan Nuwamba, Amerkawa ke gudanar da bikin yiwa Allah godiya da samun sabuwar kasar Amurka. Bikin da a turance ake kira Thanksgiving da Turanci.

Wannan ranar ta hutu ce a fadin Amurka inda Amurkawa na shakatawa tare da cin abinci da gudanar da tarukan tuntubar juna da zuwa kantuna tare da iyali domin sayen kayan marmari.

Wannan buki na cika-ciki na zuwa da al’adu iri-iri; wanda daga cikinsu shi ne tafiya a hadu da ‘yan’uwa na jini da abokai.

Kamar yadda suka saba ana haduwa da ‘yan’uwa da abokai a ci abinci, da kallon fareti da kwallon kafa da sauransu.

Hakazalika iyalai da abokai kan hadu waje guda a gasa talo-talo.

Ga wasu kuwa lokaci ne na hutu da fara yin sayayya musamman na Kirsimeti.

Ana kuma gudanar da shaharren paratin Macy Day's a fadin kasar da ka iya jan miliyoyin 'yan kallo.

Macy's Thanksgiving Day Parade in New York City

Ana kiyasin mutane miliyan 49 ne za su yi tafiye-tafiye gabanin wannan hutun, wanda hakan ya dara na bara da miliyan guda; don haka ya zama bukin cika ciki mafi armashi cikin kusan shekara 10.