Ofishin kasafin kudin majalisar dokoki da bashi da alaka da banbancin siyasa, ya fitar da wata kididdiga wacce ta nuna cewa akalla Amurkawa miliyan 22 ake tunanin za su rasa inshorar lafiyarsu nan da wasu shekaru masu zuwa idan aka amince da sabon tsarin kiwon lafiya da zai maye gurbin Obamacare.
WASHINGTON D.C. —
Ofishin kasafin kudin majalisar dokokin Amurka ya fitar da wata sanarwar wacce ta bayyana cewa Amurkawa miliyan 22 ne za su iya rasa inshorar lafiyarsu nan da shekaru masu zuwa a karkashin sabon kiwon lafiyar da da ake so a maye gurbinsa da shirin kiwon lafiya mai rahusa da Obama ya samar.
Shugaban Donaltd Trump yana kiran ‘yan jam’iyar Democrats dake adawa da tsarin "‘yan hana ruwa gudu” domin kin taimakawa ‘yan jam’iyar Republican samar da tsarin da zai maye gurbin wanda aka kafa doka a kai karkashin shugabancin Barack Obama mai taken Obamacare.
Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter jiya Litinin cewa, ‘Yan jam’iyar Demoocrats ba su da tsare-tsare ko dabaru masu kyau.
Abinda suke yi kawai shine sa kafar angulu da kuma korafi, in ji shugaba Trump.