Jiya Talata shugaban kasar Amurka Barack Obama za bayyana sabbin matakan taimakawa wajen yaki da barkewar cutar Ebola mafi munin da aka taba gani a yankin Yammacin Afirka, a ciki har da tura sojojin Amurka 3,000 zuwa yankin wadanda kwararru ne a aikin kowon lafiya.
Wata sanarwar Fadar White House ta shugaban kasar wadda ta yi bayani dalla-dalla game da shirin, ta ce za'a tura sojojin ne zuwa sabuwar cibiyar tsare-tsare ta ayyukan Amurka a Monrovia babban birnin kasar Laberiya, inda za su taimaka da sufurin kayan aiki da ma'aikata.
Haka kuma Amurka za ta gina cibiyoyin jinyar cuytar Ebola tare da sa zuba ma'aikata. Zata kuma kafa sansanin horas da ma'aikatan kiwon lafiya 500 a kowane mako.
Fadar White House ta ce burin bullo da wannan shiri shi ne shawo kan annobar cutar Ebola daga tushen ta, da takaita irin bannar da cutar za ta yiwa yankin a fannin tattalin arziki da siyasa, da kuma kafa tsarin kula da lafiya mai inganci da karko a Yammacin Afirka da ma wasu wuraren.
Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa ta Amurka ko USAID ita zata kaddamar da shirin rarraba kayan kare kai daga kamuwa da cutar, da koyawa mutane dabarun kare kansu da iyalansu. Hukumar zata fara ne da gidaje dubu 400 mafiya rauni a kasar Laberiya sannan ta fadada shirin a duk fadin kasar da ma duka yankin Yammacin Afirka.