Amurka zata tura karin dakarun sojojinta da wasu kayayyakin kariyar makamai ta sama zuwa kasar Saudiyya da kuma kasashen hadaddiyar daular Larabawa da ake kira UAE a takaice, a cewar ma’aikatar tsaron Pentagon jiya Jumma’a.
Wannan sanarwar na zuwa ne bayan harin da aka kai akan masana’antun sarrafa man kasar Saudiyya a karshen makon da ya gabata wanda jami’an Amurka suka ce Iran ce ta kai harin, zargin da ita kuma Iran ta musanta.
Shugaban Amurka Donald Trump ya amince da tura dakarun na Amurka, wadanda aikinsu shine bada kariya, a cewar sakataren harkokin tsaron Amurka Mark Esper a lokacin wata ganawa a ma’aikatar Pentagon.
Esper ya ce Amurka na daukar matakin ne saboda Kasashen Saudiyya da na UAE ne suka bukaci ta tayi hakan don inganta matakan kariyar su ta sama da kuma na makamai masu linzame bayan harin da aka kai ranar 14 ga watan Satunba.