Kasa da wata daya bayan alkawarin da shugaban Amurka Donald Trump, yayi na sayar Najeriya, wasu zaratan jiragen saman yaki, kasar Amurka, ta kara jaddada kudirinta na taimakawa Sojojin Afrika, kamar yadda kwamandan Sojojin Amurka mai kula da Afrika janar Thomas D. Waldhauser.
Wannan mataki dai na kara taimakawa dakarun Afirka, wajen yaki da aiyukan ta’addanci a nahiyar ya zo ne kasa da wata guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump, yayi alkawarin cewa amurka zata sadawa Najeriya, wasu jiragen yaki da kudinsu ya kai Dala miliyan dari shida ($600) kwatankwacin Naira miliyan dubu da dari takwas.
A cewar babban kwamanda dakarun Amurka, mai kula da Afirka, janar Thomas D. Waldhauser, mai hedkwatar a birnin Stuttgart, ta kasar Jamus, akwai yarjejeniyoyi da dama tsakanin Amurka da dakarun nahiyyar Afirka, masamman ma dai masu tabbatar da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi, inda ake fafatawa da kungiyar Boko Haram da ISIS na yammacin Afrika.
Ya kara da cewa zasu ci gaba da marawa dakarun masamman wadanda suke yankin tafkin Chadi dake karkashin Sojojin kasa da kasa wajen tabbatar da zaman lafiya dakuma ganin cewa an yaki kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu aiyukan ta’addanci a Najeriya da yankin nahiyar Afirka baki daya.
Your browser doesn’t support HTML5