Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada jiya Littini a babban birnin Kenya- Nairobi cewa Amurka zata taimakawa kasashen Africa da miliyoyin daloli.
Kerry yace akwai karin dala miliyan 45 za’a asamar domin agaza wa yan gudun hijiran nan su dubu dari 6 da suke zaune a Kenya. Kerry ya yaba wa Kenya da daukar dawainiyar wadannan yan gudun hijiran.
Sai dai tun farko Kerry ya karrama wadanda harin bomb din nan na shekarar 1998 ya rutsa dasu a ofishin jakadancin Amurka dake Nairobi, dama wasu sauran hare-haren da kasar tayi fama dasu. Kuma yayi alkawarin cewa Amurka zata ci gaba da marawa kasar baya wajen yaki da ta’addanci.
Kerry yabi sahun shugabannin kasashen waje wurin bikin aza huren kallo a kabarin wadanda suka rasa rayukan su sakamakon harin bomb da aka kai a ofishin jakadancin Amurka. Yace har kullun yan ta’adda ba zasu yi nasara ba, duk ko da kokarin su ganin sun shuka tsoro ga zukatan mutane