Kama daga arewacin Najeriya zuwa kudancin kasar labarin daya ne inda Fulani da Manoma ke yawan fafatawa.
A wani taro da wasu jami'an ofishin jakadancin Amurka suka fara gudanarwa da shugabannin Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya a karkashin jagorancin sarkin Fulanin birnin Legas kuma shugaban kungiyar Fulani a yankin, Alhaji Muhammad Banbado sun bayyana bukatar a zauna domin fahimtar juna tsakanin Fulani da Makiyaya dake zaune a yankin.
Alhaji Muhammad Banbado sarkin Fulani birnin Legas ya bayyana dalilin taron . Yana mai cewa jami'an Amurkan suna neman yadda zasu taimaka akan rikicin makiyaya da manoma a kudu maso yamma. Yace sun duba hanyoyin da kasashen waje zasu shigo domin su tabbatar rice-rikicen basu haifar da abunbuwan da basu dace ba.
Tawagar ta ofishin jakadancin Amurka ta hada da Mr.Thomas Hans babban jami'i mai kula da tattalin arziki da kuma siyasa sai kuma wasu jami'an biyu wadanda suka jaddada bukatar fahimtar juna domin a gano bakin zaren matsalar domin warwareta.
Inji daya daga cikin tawagar tace dole ne idan ana son a shawo kan matsalar a duba matsalar dake addabar manoma da kuma makiyaya wadda take da nasaba da dumamar yanayi lamarin da ya sa wasu manoma da makiyaya suna kaura daga wasu kasashe irin su Mali da Nijar da Chadi suna gangarawa kudancin Najeriya domin samun albarkar noma da kuma kiwo.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5