Amurka Za Ta Maka Haraji Ga Kashashen Da Basu Shawara Da Ita

Shugaba Donald Trump ya jadada niyarsa na ci gaba da kara haraji ga kasashen da yace suna kwarar Amurka a fannin cinikayya duk da rashin goyon bayan da yake fuskanta a ciki da wajen kasar

Shugaban Amurka a yau Talata yayi barazanar maka haraji ga kasashen da basu yin shawara da kasar Amurka da zuciya daya inda yake cewa sune hanyar warware matsalar cinikayya ta duniya.

Haraji babban abu ne Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na twitter. Abu ne mai sauki duk kasar da ba za ta yiwa Amurka adalci ba a harkar cinikayya, to za ta hadu da haraji, kuma kowa yana magana, ku tuna ,mune asusun da ake cuta. Komi zai zo dai dai.

Wannan bayani na Trump yazo ne jim kadan bayan ministan harkokin kasar Jamus Heiko Maas yace Turai ba zata ji tsoron barazanar Trump ba.
Jami'an Tarayyar Turai sun ce duk da harajin da suke ansa akan shigo da motoci sun fi na Amurka, harajin kasar Amurka wanda ya hada da manyan motoci da sauran kayyayaki yafi yawa. Tarayyar turan ta kara da cewa cire kudin shigar da motoci zai faru ne kawai idan aka kara fadada yarjejeniyar kasuwanci.