Amurka Zata Kori Wasu Bakin Haure Da Suka Fito Daga Kasashen Latin Amurka

Domin nuna rashin amincewarus da manufofin shugaba Obama kan shige d a fice wasu mutane suka yi maci zuwa ofishin hukumar shige da fice, a baya can.

Wadannan sun hada da uwaye mata da 'yayansu wadanda aka baiwa umarnin su fice.

Anan Amurka jami'an shige da fice, dana hukumar kastam, zasu kai somame cikin wannan wata da kuma watan Yuni, da zummar tusa keyar bakin haure daga kasashen Latin da suke tsakiyar nahiyar Amurka, wadanda suka shigo Amurka ba bisa ka'ida ba, kuma sun kammala daukaka kara ba tareda sun sami nasara ba.

Matakin na tsawon wata daya, zai fi maida hankali ne kan uwaye mata da 'yayansu, wadnada tuni aka basu umarnin barin kasar.

Haka nan matakin zai kuma hada harda matasa wadanda suka shigo Amurka tun suna kanana ba tareda wani babba ba,kuma yanzu sun kai shekaru 18.

A cikin wata sanarwa, kakakin kwamitin da ake kira ICE a takaice Jennifer Elzea, tace "tilas hukumar tsaron cikin gida ta Amurka,ta tabbatar da an mutunta doka, kamar yadda aikin ya tanadar.