Gwamnatin shugaba Trump na kara sanya takunkumi akan jami’an Rasha da wasu hukumomin kasar, akan batun katsalandan da ake zargin kasar ta yi a zaben Amurka na shekarar 2016, da kuma abinda ma’aikatar baitulmalin Amurka ta kira “miyagun ayyuka.”
Ayyukan sun hada da zargin yinkurin kashe tsohon jami’in leken asirin Rasha, da diyarsa a Burtaniya ta hanyar sa masu guba.
“Amurka zata ci gaba da aiki da kasashe kawayenta, wajen daukar matakin hadin gwiwa don dakilewa, da kuma kare ci gaban miyagun ayyukan Rasha da wakilanta, da kuma hukumomin leken asirinta,” a cewar sakataren baitulmalin Amurka Steve Mnuchin.
Cikin wadanda aka sanyawa takunkumin harda jami’an leken asirin soja guda 15, da wasu kamfanonin gwamnatin kasar guda 4, ciki harda wata cibiyar binciken yanar gizo ta kasar.