Yanzu haka an kama mutane 30 dake da alaka da harin da aka kai a Habasha, wanda, Shugaba Abiy ya bayyana a matsayin “shiryayyen hari ne”.
WASHINGTON D.C —
Kafar yada labaran kasar Habasha,Fana Broadcasting Corporation, ta ce Amurka zata tura jami’an hukumar binciken manyan laifuffuka ta FBI don su gudanar da bincike akan wani mummunan harin bam da aka kai a birnin Addis Ababa ranar Asabar din da ta gabata.
Sakataren ma’aikatar harkokin cinikayyar Amurka, Gilbert Kaplan yayi wannan bayanin ne yau Litinin bayan ganawarsa da ministan harkokin wajen Habasha.
An kashe mutane biyu yayinda wasu 150 kuma suka jikkata a harin gurneti da aka kai bayan da sabon Firai minista mai neman kawo canji, Abiy Ahmed ya kamala wani jawabi gaban dubban magoya bayansa.
Yanzu haka an kama mutane 30 dake da alaka da harin da aka kai a Habasah, wanda, Shugaba Abiy ya bayyana a matsayin “shiryayyen hari ne.