Amurka Za Ta Taimaka wa Najeriya Wajen Inganta Tsaron Cikin Gida

US-Nigeria Security meeting in Abuja

A wani taron hadin gwuiwa tsakanin shugabannin tsaron Najeriya da ministan cikin gida Janar Abulrahman Dambazzau, da Jakadan Amurka a Najeriya da aka yi a Abuja, bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin tsaro domin kasar ta samu cikakken zaman lafiya.

Jakadan Amurka a Najeriya, Stuart Symington, ya ce tsaron Najeriya da ci gaba da kasancewa kasa daya, na da mahimmanci kwarai a nahiyar Afirka.

Symington ya bayyana hakan ne, yayin wani taron hadin gwuiwa tsakanin Amurka da Najeriya a Abuja.

Jakadan Amurkan ya ce ya yi farin cikin ganin yadda shugabannin rundunonin tsaron kasar suka hadu wuri guda domin tattauna sha'anin tsaro.

A cewar Symington, Amurka za ta tallafawa Najeriya da irin dabarun da ta bi ta samu nasara domin ita ma Najeriya ta kai wannan mataki.

Ana shi bangaren, Janar Dambazzau mai ritaya, ya ce tsaro da zaman lafiya su ne abubuwan da gwamnatinsu ta sa a gaba saboda haka samun nasarar shirin zai ta'allaka ne a hannunsu gaba daya.

Aliyu Ibrahim Gebi wanda ya kasance jagoran shirin tsakanin Najeriya da Amurka, ya ce ganin yadda abubuwa ke faruwa a yankin arewa maso gabas ya sa gwamnatin Amurka ta zabura wajen ba da wannan tallafi.

Saurari rahoton Hassan Maina Kaina domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Inganta Tsaron Cikin Gida- 2' 46"