Jakadan Amurka a Najeriya ya kai wata ziyara ta musamman jihar Zamfara, inda ya gana da duk masu ruwa da tsaki, don gano hanyar da Amurka zata iya taimakawa don shawo kan tashin hankalin da ake fama da shi a jihar Zamfara.
A tsawon kwanaki biyu da ya kwashe yana ziyara a jihar Zamfara, jakadan Amurka a Najeriya David Young, ya sami tattaunawa da gwamna da manyan jami’an gwamnatin jihar da sarakunan gargajiya da ‘yan Majalisar Dokoki, da ma kungiyoyi da kabilu daban-daban.
Sai dai Mista Young ya ce ya lura matsalar tashe-tashen hankali a jihar Zamfara, ta banbanta da dukkan matsalolin tsaro da ake fama da su a wasu sassan Najeriya.
Akan haka ya ce gwamnatin kasar Amurka a shirye ta ke ta bayar da tallafin hadin gwiwa domin magance ta’addanci a jihar. Yanzu haka dai Amurka na tallafawa Najeriya zunzurutun kudi har dala miliyan dubu ‘daya a kowacce shekara, domin yaki da matsalar tsaro.
A cewar jakadan Amurka Mista Young, ziyarar da suka kai jihar Zamfara ta ‘kara tabbatar da irin kakkarfar hadin gwiwa dake akwai tsakanin Amurka da Najeriya, da kuma hadin gwiwar jama’ar kasar, domin kuwa kowanne ‘dan Najeriya yana da muhimmanci haka kuma kowacce rayuwa muhimmiyace.
Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5