Amurka Za Ta Sabunta Yarjejeniyar Sassauta Takunkumin Iran

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad a ma'aikatar nukiliya

Gwamnatin Donald Trump ta fitar da sanarwar cewa za ta ci gaba kan tsarin yajejeniyar da ta sassauta takunkumin da aka kakabawa kasar Iran, wanda aka samar tun lokacin mulkin Obama.

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma ta shekarar 2015, an dage takunkumin da aka kakaba ma Iran kan shirin ta na Nukiliya, idan har Iran din ta amince ta dakatar da shirin Nukiliyarta. Amma yarjejeniyar tana bukatar duk watanni shida sai an sabuntata.

Ta baya bayan nan da aka sabunta itace wadda tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi, kuma cikin wannan makon wa’adin yarjejeniyar zai cika.

Amma kuma gwamnatin Amurka ta ‘kara sakawa wasu jami’an Iran takunkumi har biyu, wani kamfanin Iran da wani kamfanin China dake taikamakawa makaman Iran.

A cewar babban jami’in diplomasiyar Amurka a gabas ta tsakiya, Stuart Jones, “idan Iran ta ci gaba da kera makamai har sukai ga makaman Nukiliya, su sani da cewar hakan ya sabawa kudurin da kwamitin sulhun MDD ta samar.

Haka kuma ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wani rahoto da ke sukar ‘kasar Iran kan take hakkin bil Adama.