Amurka: 'Yan takarar Democrats Clinton da Sanders sun yi jayayya akan akidojinsu

Clinton da Sanders 'yan Democrats dake neman shugabancin Amurka a zabe mai zuwa

'Yan takarar Shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Democrat Hillary Clinton da Bernie Sanders, sun yi jayayya da juna game da akidojinsu a siyasance, a wani zama na musayar ra'ayi da jama'a, wanda aka yada ta gidan talabijin a New Hampshire da daren jiya Laraba.

Sanders, wanda ke bayyana kansa a matsayin dan Democrat mai ra'ayin gurguzu, wanda ya fito makwabciyar jaha ta Vermont, ya jefa ayar tambaya kan yanayin akidar sassauci ko ta gaba-dai-gaba-dai ta tsohuwar Sakatariyar, musamman game da batun sa ido kan harkokin Wall Street, da sauye-sauye game da kudaden da ake kashewa kan yakin nemar zabe da kuma yadda, a shekarar 2003 ta kada kuri'ar amincewa da mamayar Iraki lokacin ita ce 'yar Majalisar Dattawa mai wakiltar Jahar New York.

Ita kuwa Clinton cewa ta yi abokin karawar na ta, "ya nada kansa a matsayin mai tantance ko waye cikakken dan ra'ayin gaba dai- gaba dai ," kuma bisa ga wannan mizani nasa, ko shi kansa Shugaba Barack Obama ko Mataimakin Shugaban kasa Joe Biden bai cikin wannan rukunin. Ta kara da yadda ta yi ta gwagwarmaya kan abubuwan da su ka hada da kiwon lafiya.

Zaman na jiya Laraba, ya zo ne kwanaki biyu bayan da Cliton ta yi galaba da kyar kan Sanders a zaben fidda dan takara da aka yi a Iowa, wadda ita ce jahar farko wajen kada kuri'ar zaben dan takara a zaben Shugaban kasa na shakarar 2016.