Amurka Tayi Watsi Da Sauye Sauyenda Mubarak Ya Gabatar

Kakakin fadar White House Robert Gibbs,yake magana da manema labarai gameda hali da ake ciki a Masar.

A dai dai lokacinda shugabannin kasashen Duniya suka zuba ido suna kallon rudani a Masar, Amurka ta yi watsi da kafa sabuwar gwamnati da shugaba Mubarak, dake “tsakawa mai wuya” yayi.

A dai dai lokacinda shugabannin kasashen Duniya suka zuba ido suna kallon rudani a Masar, Amurka ta yi watsi da kafa sabuwar gwamnati da shugaba Mubarak, dake “tsakawa mai wuya” yayi. Washington tana cewa lamarin yana bukatar daukar matakai, ba nade-nade ba.

Kakakin fadar White House,Robert Gibbs ya fada litinin cewa,Amurka tana kira ga “sauyi gameda yadda ake tafiyar da mulkin kasar”,sai dai bace Mr.Mubarak ya yi murabus ba.

Gibbs yace Washington tana son ganin an gudanar da “shawarwari sahihi”tsakanin dukkan kungiyoyin Masar. Ya sake nanata kiran gwamnatin Obama na ganin an gudanar da zabe sahihi. Ya kara da cewa ba Amurka ce zata kudura,ko ta tursasa lokaci da yanayin canji a Masar ba.

Jami’an fadar white,suka ce Amurka tana matsawa Mubarak lamba ya gabatar da sauye sauye a matakin farko na biyan bukatar masu zanga zanga dake neman ganin bayansa.Matakan su hada da dage dokar tabaci,da sakarwa kungiyoyin masu zaman kansu mara,da kuma sakin dukkan fursinonin siyasa.

Washington ta tura wani manzo na musamman,tsohon jakadan Amurka a Misra,Frank Wisner, domin ya tattaunawa da manyan jami’an Masar kan bukatar aiwatarda sauye sauye kan tafarkin Demokuradiyya.

Amurka ta juma tana goyon bayan Mubarak,tana kallonsa a matsayin aboki ga Isra’ila, kuma garkuwa daga masu matsanancin ra’ayin Islama.

Da yake magana litinin din nan,PM Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadin hadarin sai tayu a sami gwamnati mai bin tafarkin addini,shigen abinda ake da shi yau a Iran a Masar.

Tunda farko litinin din nan,babbar jakadiyar tarayyar Turai ta yi kira ga shugaban na Masar da ya maida martani kan koke koken masu zanga zanga,kuma ya yi shawarwari da su.