Amurka Tana Kokarin Warware Rikici Tsakanin Wasu Kasashen Yankin Gulf Da Qatar.

Sakatare Tillerson da shugaba Erdogan na Turkiyya.

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson wanda ya ziyarci Turkiyya da Kuwait zai kuma yada zango a Saudiyya.

Yanzu haka sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya na kasar Kuwait a kokarin taimakawa wurin warware takaddama tsakanin Qatar da makwabtarta a yankin Gulf.

Haka kuma an shirya Mr. Tillerson zai kai ziyara a Saudiya da kuma Qatar a cikin wannan mako.

A jiya Litinin Tillerson ya gana da shugaban Turkiya Recep Erdogan, bayan ziyarar daya kai kasar Ukraine a ranar Lahadi.
Kafin ya bar Turkiya zuwa Kuwait, babban mai bada shawara a kan sadarwa R.C.Hammond yace babban manufar ziyarar Tillerson zuwa kasashen yankin Gulf itace neman hanyar warware wannan rikici.