Amurka tana kara inganta matakan tsaro a jiragen saman dake shigowa kasar

wurin bincike a tashar jirgin sama

Amurka tana kara inganta matakan tsaro a jiragen saman dake shigowa cikin kasar a daukacin tashoshin jiragen saman kasa da kasa dake cikin Amurkan

Sai dai a halin yanzu bata karfafa dokar hana daukar kumfutar hannu ba wato LAPTOP.

Sai dai kuma Sakataren tsaron cikin gida John Kelly ya fada jiya laraba cewa, kada ayi sake domin ko har kullun makiyan su, na nan, na kokarin samar da wasu sababbin hanyoyin boye nakiyoyi tare da anfani da wadansu ‘yan cikin gida da kuma satar jiragen sama.

Kelly yace za a dauki sababbin matakai da wadanda matafiya suka gani da kuma wadanda ba su gani ba, nan da ‘yan watanni.

Yace don haka matafiya su sa ran cewa za a kara tsawaita bincike ko kuma tantancewa da naurori, haka kuma za a kara yawan jami’an tsaro a kowane jirgin sama da tashoshin jiragen sama baki daya, kana za a samar da karnuka masu gano boma-bomai da sinadarai.