Amurka Tace Bata Da Tabbacin An Kashe Shugaban Kungiyar ISIL Abubakar Al-Baghdadi

Abu Bakr al-Baghdadi, Shugaban Kungiyar ISIL a Birnin Mosul.

Yayin da Rasha ta sanar da cewar ta kashe shugaban kungiyar ISIL Abu Bakr Al-Baghdadi da wasu manyan kwamandojin na ISIL Amurka na tababan hakan.

Masu fashin bakin al’amurran tsaro da leken asiri na nuna rashin amincewa da rahotannin da ake watsawa cewa an kashe shugaban kungiyar ISIL Abu Bakr al-Baghdadi a wani hari da aka kai ta sama cikin watan da ya gabata.

Mai magana da yawun dakarun dake yaki da kungiyar ISIL, Col. Ryan Dillon, ya ce Amurka ba zata iya tabbatar da gaskiyar rahotan ba a wannan lokaci.

A yau Juma’a ne rundunar sojan Rasha ta ce wani hari da suka kai ta sama a Syria kan shugabannin kungiyar ISIL a karshen watan Mayu, da alamu an kashe shugaban.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Tsaron Rasha ta bayar a shafin Facebook, na cewa harin da aka kai ta sama a birnin Raqqa ya fada taron da shugaban ISIL al-Baghdadi ya jagoranta.

Rasha dai ta yi da’awar cewa harin ya hallaka wasu shugabannin kungiyar, da suka hada da kwamandoji 30 da mayakansu wajen 300.

Rundunar sojan Rasha dai tace tana bincikar hanyoyi daban-daban a kokarin gano ko da gaske ne an kashe al-Baghdadi.