Kayayyakin da Amurka ta ba Jamhuriyar Nihar taimako sun hada da da jiragen samun bayanai da jiragen hango abokin gaba guda biyu.da kuma motocin sojoji guda talatin da uku.
Idi Barau jami’in dake kula da harkokin sadarwa a ofishin jakadancin Amurka dake birnin Nyamie yace kudin motocin kadai ya kai saifa biliyan bakwai, jiragen da kayan aikin da suke dauke da su kamar kamarori, da na’urorin dake basu damar hango abokan gaba, sun kai kudi saifa biliyan goma sha uku.
A nasa bangaren ministan Muhammadu ya yaba matuka da taimakon na Amurka, yace kasar Amurka ta nuna a zahiri niyyarta ta taimakawa Jamhuriyar Nijar, a karshen jagorancin shugaban kasar Yusuf Muhammadu da kayayyakin aiki na sojoji, domin kara basu damar tabbatar da tsaron iyakokinmu da al’umma da kuma kaddarori
Za a kai kayan na sojoji ne a yankin Durku, wadanda sojojin zasu yi amfani da su, wajen samun bayan da suka shafi tsaro.
Daga Nyamai, ga Rahoton wakilin Sashen Hausa Yusuf Abdullahi.
Your browser doesn’t support HTML5