Amurka Ta Zauna Kan Teburin Tattaunawa Da Kungiyar Taliban

Mike Pompeo

Kungiyar Taliban ta tabbatar da tattaunawa da Amurka kai tsaye a Qatar a cikin wannan mako da zummar kawo karshen yakin shekaru 17 a Afghanistan.

Wani babban jami’in Taliban ya fadawa wakilin Muryar Amurka a jiya Juma’a cewa, Alice Well mukaddashiyar sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da Kudu da Tsakiyar Asia, itace ta jagoranci tawagar Amurka a wajen tattaunawar a birnin Doha.

Jami’in kungiyar ta yan ta’addar da bai so a bayyana sunansa ba, ya yi bayani cewa, a zaman farkon bangarorin biyu sun duba yadda za a shirya tattaunawa nan gaba da kuma wadanda zasu zama wakilan Taliban da Amurka.

Lallai an samu yanayi mai inganci a tattaunawar farkon kuma zaman ta yi mana’a, inji jami’in na Taliban, sai dai bai yi wani karin bayani ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka taki cewa uffan a kan batun ganawar da Amurka ta yi da kungiyar ta’addanci ta Afghanistan.