Amurka Ta Yi Ikrarin Kashe 'Yan Ta'adda 15 a Somalia

Wani yanki da aka yi bore e Somalia a bara

Wasu hare-haren sama da dakarun Amurka suka kai a Somalia, sun halaka mayakan Al Shabab 15 da ke yaki da dakarun Afirka da na Somalia.
Kakakin rundunar dakarun Amurka ta AFRICOM da ke Afrika, Manjo Karl Wiest ne ya fadawa Muryar Amurka a karshen makon nan.
A cewar shi, mayakan na zama "babbar barazana" ga dakarun kasa da kasa, wandanda jami'an tsaron Amurka suka ce sun yi nasarar kwato garin Janaale da ke yankin Lower Shabelle.
Rundunar ta AFRICOM har ila yau ta fada a wata sanarwa da fitar cewa, ta kai wasu hare-hare guda biyar a tsakanin Litinin da Talata a kusa da yankin Janaale tare da hadin gwiwar gwamnatin Somalia.