Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Karin Wa’adin Mulki

The White House

Wa’adin mulkin shekaru hudu a matsayin shugaban kasar Somalia naMohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmaajo, ya kare ne a ranar 8 ga watan Fabrairu, amma ya ci gaba da kasancewa a kan mukaminsa saboda doguwar rashin jituwa da shugabannin kungiyar mambobin Tarayyar kasar kan yadda za a gudanar da zabe.

A ranar 12 ga Afrilu, karamar majalisar dokokin Somaliya ta jefa kuri’ar yadda za a kara wa’adin Gwamnatin Tarayya da na Majalisar da shekaru biyu, abin da ya kawo cikas ga hanyoyin da za a bi don warware matsalar da kuma gudanar da zabe nan take. Kwana daya bayan hakan, Shugaba Farmaajo ya sanya hannu kan kudirin.

Kasashen duniya, ciki har da Amurka, suna adawa da karin wa’adin,da suka bayyana a matsayin babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Somaliya da makwabtanta, suna masu gargadin cewa kungiyar ta’addanci ta al-Shabaab za ta iya amfani da wannan rarrabuwar kawuna da ke haifar da hakan.

Amurka da wasu a cikin kasashen duniya suna kuma yin gargadin cewa tsawaita wa’adi da ci gaba da rashin jituwar siyasa zai kawo cikas ga shugabannin Somalia don biyan bukatun mutanen Somaliya.

Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, "Mun bayyana a fili cewa Amurka ba ta goyon bayan karin lokaci ba tare da samun cikakken goyon baya daga masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa na Somaliya ba, haka kuma Amurka ba ta goyon baya ga tsarin zaben da ake gudanarwa dabam dabam ko kuma rabi da rabi."

“Irin wadannan ayyuka za su kasance masu rarraba kai sosai, su lalata tsarin tarayya da sake fasalin siyasa wadanda suka kasance tushen ci gaban kasar da kawance da kasashen duniya, da kuma karkatar da hankali daga dakile ayyukan al-Shabaab. Haka nan kuma za su kara jinkirta gudanar da zabubbukan da aka yi alkawalin da mutanen Somaliya ke jira. ”

Sakatare Blinken ya yi gargadin cewa Amurka na iya sanya takunkumi da hana biza. Har ila yau Amurka na iya sake nazarin taimakon da Amurka ta ba Somalia, kasar da ta dogara sosai kan taimakon waje don bukatun yau da kullum kamar abinci, da kuma horarwa da kuma samar da kayan aiki ga jami'an tsaronta.

Sakatare Blinken ya yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Somaliya da shugabannin mambobin Tarayyar da su koma kan teburin tattaunawa da nemo hanyar warware rikicin zabe.

"Muna kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsan-tsan, su ci gaba da tattaunawa, kuma su guji ci gaba da daukar matakai na bai daya wanda zai ruruta wutar rikici da kuma lalata tsarin dimokiradiyya na Somaliya da ma cibiyoyinta.