Amurka Ta Tsanata Matakan Tsaro Sabo Da Ana Shirin Kawo Mata Hari

Jami'in tsaro a New York.

Magajin garin birnin New York Michael Blomberg yace an kara tsananta matakan tsaro cikin birnin domin bayanai masu sahihanci da aka samu duk da cewa ba’a tabbatar hakikanin inda ake auna kai harin ba.

Magajin garin birnin New York Michael Blomberg yace an kara tsananta matakan tsaro cikin birnin domin bayanai masu sahihanci da aka samu duk da cewa ba’a tabbatar hakikanin inda ake auna kai harin ba, da aka kitsa domin yazo dai dai da cikar shekaru 10 da kawowa Amurka harin ta’addanci da aka yi ranar 11 ga watan satumban 2001.

Da yake magana a taron manema labarai a daren jiya Alhamis, kwamishinan ‘yansanda na birnin New York Ray kelly yace karin matakan tsaro da za a dauka sun hada da wuraren duba motoci a kewayen birnin na New York, duba jakakkunan masu shiga jiragen kasa, da jami’an tsaro da karnuka da suke iya gano boma bomai d a na’urori na musmaman na gane makamai masu hadari wadanda za’a girke a sassa daban daban cikin birnin na New York. Kwamishina Kelly yace ‘yansanda zasu fi maida hankali kan hanyoyin karkashin kasa, gadoji, gine ginen gwamnati da kuma wasu muhimman wurare, da suka hada dana ibada.

Magajin garin na New York Bloomberg, yayi kira ga mazauna birnin New York dasu maida hankali su bude ido da kasa kunne.

Jiya Alhamis jami’an Amurka suka bada labarin sun sami bayanai masu sahihanci kan ana kitsa kaiwa biranen New York da Washington DC hari. Jami’ai suka ce ana zargin mutane uku da suka shigo Amurka cikin watan jiya, daya daga cikinsu ba Amurke ne, sun shigo da nufin kai hari da mota da aka dankarawa boma-bomai.

Fadar White House tace ana ci gaba da baiwa shugaba Obama karin bayani kan shirin ta’addanci a duk wunin jiya. Dagan an shugaban ya kara kira ga jami’an yaki da ta’addanci su kara himma wajen kare Amurka daga duk wani hari.