Amurka Ta Taimakawa Jamhuriyar Nijar Da Kudi

  • Ladan Ayawa

Yarjejeniyar Amurka Da Jami'ar ESCAE

Kasar Amurka ta hanyar tsarin ta da ake kira MCC ta taimakawa jamhuriyar Niger da makuddan kudade n da yawan su yakai sefa Miliyan dubu 225.

Kuma daga cikin wadannan kudaden shugaban kasar Jamhuriyar ta Niger ya kebe miliyan dubu 43 dominn sake farfado da dam kogandarin garin birnin konni dake da kewaye da gonaki dubu 3.

Shi dai wannan dam din yana kawo kyakkyawar gudun mowar sa wajen rage matsallar abinci a kasar ta Jamhuriyar Niger. Domin ana noma a lokutta biyu wato rani da damina.

Kamar yadda Alhaji Umaru zakari dan majilisar dokokin mai wakiltan mazabar birnin Konni yayi bayanin zaman da akayi da shugaban hukumar ta MCC a birnin konni.

‘’An turo babban darekta na babban hukumar nan da ake kira MCC ya kawo wa jamaar birnin konni albishir kuma yazo ya tambayi jamaar kasar Konni su dauki alkawari cewa wannan aikin da za ayi zasu dauke shi da hannu bibbiyu domin aci nasarar sa’’.

Yace zaman da suka yi sunyi shine da sarakuna da shugabannin al’umma daban-daban.

Ga dai Haruna Mammam Bako da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

AMURKA TA TAIMAKWA JAMHURIYAR NIGER DA KUDI. 3'23