Amurka ta sanar da kashe Abu Wahib wani shugaban kungiyar ISIS

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter

Ma’aikatar tsaro ta Pentagon anan Amurka, ta ce an kashe wani takadarin jagoran kungiyar ISIS dake lardin Anbar a kasar Iraki tare da wasu mayakan sa kai guda uku, a wani farmaki ta sama da sojojin taron dangi suka kai.

Kakakin ma’aikatar ne Peter Cook ya bayyana haka a jiya Litinin, yace harin ranar 6 ga watan nan na Mayu ne ya auna tare da tarwatsa tawagar motocin jagoran mai suna Abu Wahib tare da wasu mataimakansa a kusa da garin Rutba.

Cook ya alakanta Abu Wahib a matsayin wanda yake shirya da wallafa bidiyon da ISIS ke yadawa na kisan gillar da takewa mutane, sannan kakakin na Pentagon yace, wannan kisa na ‘yan ta’addan wani ci gaba ne a yakin kawar da kungyar ISIS daga fadin duniyar nan.

Musamman a matsa lambar da gwamnatin Iraki da sojojin taron dangin da Amurka ke jagoranta ke yi akan yaki da ta’addanci. Sai dai Mista Cook bai fadi ko jirgin yakin soji ne mai matuki ko kuma mara matuki ne ya kai harin ba.

Sannan bai alakanta wata hujja da ta shafi rahoton gwamnatin Iraki ba na shekarar 2015 kan cewa, ta kashe dan ta’addar. Shafin yanar gizon Kurdawa da ‘yan Shi’a ya bayyana cewa Abu Wahib na cikin wadanda suka tsere da fursuna Tikrit mai tsananin tsaro a shekarar 2012.