Wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, ya ce, Amurka ta dade ta na sukar yiwa tarin mutane shari’a da yanke hukunci a lokaci guda, wanda ya ce hakan ya sabawa nauyin kasa da kasa da ya rataya a wuyan kasar ta Masar da kuma tsarin bin doka.
A jiya Asabar kotun wacce ta yi zamanta a birnin Alkahira ta yanke hukuncin.
A kuma ranar 2 ga watan Yuni, babbar hukumar da ke kula harkokin addinin kasar ta Mufti, za ta bayyana matsayarta kan wannan hukunci.
Yanzu haka, lauyan Mr Morsi, ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kisan, yayin da masu goyon bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim brotherhood ke kiran a fito a yi zanga zanga.
Har ila yau kotun ta yanke hukunci akan wasu manyan kungiyar, wadanda aka same su da laifin hada kai da ‘yan kungiyar Hamaz da Hizbullah wajen fasa gidan yarin.