Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce ta maida hankali sosai domin ganin an maido da ayyukan ba da agaji a arewacin jihar Rakhine da ke Myanmar, tana mai cewa ta damu matuka da zargin da ake yi na keta hakkin bil adama a yankin.
Yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ta wayar talho, Mataimakin Sakataren harkokin wajen Amurka a yankin Asiya, Patrick Murphy, ya ce Amurka na kira ga bangarorin da abin ya shafa, da su kwantar da hankula, yana mai cewa tun daga watan Agusta, kusan ‘yan gudun hijira dubu 200, suka tsallaka zuwa kasar Bangladesh, domin tserewa rikicin.
Ya kara da cewa, ba a san adadin mutanen kuma da suka fice daga gidajensu ba, wadanda suna nan a cikin kasar, sai dai ya ce wadanda aka tilastawa ficewa daga gidajensu akwai Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da sauran wadanda ba ‘yan kabilar ba.
A wani labari na daban, yayin da dubun dubatar ‘yan kabilar ta Rohingya wadanda Musulmi ne ke ficewa daga jihar ta Rakhine zuwa Bangladesh sanadinyar hare-haren da mabiya addinin Buddha ake zargin suke kai musu, masu fashin baki, sun yi gargadin cewa a yi hattara, domin wannan rikici zai iya zama wata kafar da za a samu masu ta da kayar baya daga kasar waje, idan har ba a dauki mataki ba.
Masu fashin bakin sun ce, masu ta da kayar bayan za su iya amfani da ‘yan kabilar ta Rohingya da ake muzgunwa wajen diban sabbin mayakansu.
A cewar mai fashin baki kan harkar tsaro, Hassan Askari da ke zaune a Pakistan, yayin wata tattaunawa da ya yi da Muryar Amurka, ya zuwa yanzu babu wata shaida da ta nuna cewa akwai mayakan Alqaeda ko kuma na IS a kasar ta Myanmar, amma kuma an ga kungiyoyin sun fitar da sanarwar nuna jajensu ga ‘yan kabilar ta Rohingyan.
Saboda haka a cewar Askari, idan lamarin ya kara tabarbarewa, babu makawa akwai yiwuwar samun bullar mayakan ‘yan ta’adda a yankin, ta yadda har za su iya shiga kasar ta Myanmar.