Jakadun Amurka 'Yan Siyasa Suyi Murabus Nan Da 20 Ga Watan Janairun Nan.

John kirby, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka.

Fadar White House ce ta ada wannan umarni ranar Jumma'a.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta umarci dukkan jakadun kasar wadanda suka san cewa su 'yan siyasa ne su mika takardar barin aiki nan da 20 ga wanan wata, ranar da sabon shugaban kasa zai kama aiki.

"Wannan itace al'adar" inji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka John kirby, jiya Jumma'a, inda ya tabbtar da cewa jakadun Amurka wadanda ba 'yan siyasa ba, sune kusan kashi 70 cikin dri na jakadun kasar a ketare, zasu ci gaba da aikinsu a inda suke.

Amma a karkashin wannan umarni,shine bayanai da aka bayyana cewa, jami'ai masu shirye shiryen karbar mulki na shugaba mai jiran gado su suka auke da sako ta kafofin difilomasiyya suka umarci illahirin 'yan siyasa da aka nada jakadu karkashin gwamnatin Obama su tabbata sun mika takardun barin aiki nan da 20 ga wa, mataki da jaridan New York Times tace,ya saba da ala'da inda ake barin irin wadannan jami'ai na wani dan karamin lokaci saboda wasu dalilai da ba'a rasa ba, kamar a kai ga kammala zangon karatu na yara, ko wani batu na kiwon lafiya da dai sauransu.

Amma jami'an gwamnatin mai jiran gado suka ce babu wata manufa ta gayya cikin wannan lamari.