Amurka Ta Na Tare Da Ukraine

The White House

Kasar Amurka ta damu da irin tashe-tashen hankalin da Rasha ta kara yi, a kwanan nan, a gabashin Ukraine, da kuma rahotanni game da kara yawan sojojin Rasha a kan iyakokin Ukraine da kuma Crimea da aka mamaye.

A wani taron manema labarai, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ned Price ya ce, rikicen-rikicen dakarun Rasha, ya fara ne da keta haddin yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Yulin 2020 tsakanin Ukraine da Rasha. Abin da ya yi sanadiyar mace-mace a watan Maris na sojojin Ukraine su huɗu da kuma raunata wasu ma’aikatan Ukraine guda biyu. An kuma samu karin wasu 'yan kasar Ukraine 8 da suka mutu a cikin watan Afrilu.

"Mun bukaci Rasha da tayi bayani kan wadannan tsokane-tsokanen, amma abin mahimmancin da muka nuna kai tsaye tare da abokan tarayyarmu ta Ukraine, sako ne na samun tabbaci.”

Rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine a yanzu ya fara ne a shekarar 2014 yayin da Rasha ta kwace, da mamayewa, da kuma yunkurin karbe yankin Crimea, kuma fadan ya ci gaba tsakanin sojojin Ukraine da sojojin da Rasha ke jagoranta wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 13,000, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Mai magana da yawun Price ya ce a yayin da Rasha ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a kwanan nan da kuma tarin sojoji a kan iyakokin Ukraine da Crimea da aka mamaye, jami’ai daga ko’ina cikin Amurka sun tattauna da takwarorinsu na Ukraine don jaddada goyon bayan Amurka ga ‘yancin Ukraine da kuma yankinta.

Sakonsu shi ne cewa Amurka "za ta damu da duk wani yunkuri daga bangaren Moscow, ko da a yankin Rasha, ko kuma a cikin Ukraine - don tsoratar da abokan tarayyarmu Ukraine."

"Muna tare da Kyiv," in ji Mista Price, "yayin da ake fuskantar tsoratarwa."