Amurka Ta Musanta Rufe Ofishin Jakadancinta Na Abuja, Legas

Wani mutun yana wucewa ta gaban ofishin jakadancin Amurka da ke yankin Hong Kong a ranar 2 ga watan Afrilun 2003

Ofisoshin jakadancin Amurka da ke Abuja da Legas a Najeriya, za su ci gaba da kasancewa a bude, a wannan lokaci da aka rufe wasu ma’aikatun gwamnatin Amurka, in ji wata sanarwa da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na yanar gizo.

A jiya Talata, jaridun Najeriya da dama, sun ruwaito cewa ofishin jakadancin na Amurka da ke Abuja da karamin ofishinsa da ke Legas, sun kasance a rufe sanadiyyar takaddamar rufe ma’aikatun gwamnatin Amurka da aka yi a karshen watan Disambar bara.

Sun kuma ruwaito cewa, wannan mataki ya shafi harkar bayar da takarun Visa ga masu shirin zuwa kasar a Najeriya.

Amma ofishin jakadancin na Amurka da ke Abuja, ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a yau Laraba cewa, “wadannan rahotanni kuskure ne.”

Sai dai sanarwar ta ce, “cibiyoyi da ofisoshin bai wa dalibai shawara karkashin shirin ilimi na EducationUSA da ke ofishin jakadancin Amurka da karamin ofishinta, wadanda ke karkashin kulawar bangaren harkokin jama’a, za su kasance a rufe a daukacin lokacin da aka rufe ma’aikatun gwamnatin.”

Amma sanarwa wacce aka wallafa, ta ce bangaren da ke kula da shirin nan na tabbatar da mulkin dimokradiyya da ‘yancin fadin albarkacin baki na American Spaces da ke gudana a wajen ofishin jakadancin da karamin ofishin, “zai kasance a bude.”

A yau aka shiga yini na 12 da rufe wasu ma'aikatun gwamnatin Amurka sanadiyyar takaddamar kasafin kudi tsakanin shugaba Donald Trump da 'yan majalisar dokokin kasar.

'Yan majalisar sun ki saka bukatar shubaga Trump da ya gabatar masu ta neman dala biliyan 5 domin gina katanga a tsakanin Amurka da Mexcio a cikin kasafin, shi kuma ya ki sa hannu a kasafin, lamarin da ya kai ga rufe wasu ma'aikatun na gwamnati.