A wata sanarwa da ya fitar, ofishin jakadancin Amurka ya yi kira ga ‘yan Najeriya a suyi watsi da jita-jita da kuma labaran karya, musanman a wannan lokaci na zaben kasa domin kaucewa har gitsi.
Ofishin jakadancin har ila yau, ya ce yata goyon bayan kowanne dan takara ko jam’iyyar siyasa, abin da yake kokarin yi shine tabbatar da anyi adalci ga kowa a bisa tafarki irin na Demokiradiya.
Amurka ta tunasarwa yan Najeriya cewa ita kawa ce ga Najeriya da ke son ci gaban ta, tare da bata gudunmawa na miliyoyin daloli, kudaden da kuma ke tallafawa wajen raya kasa da ci gaban al’umma kimanin miliyan biyu.
Alhaji Musa Jikanwani, mai sharhi ne akan harkokin yau da kullum kuma wakili a kungiyar Amnesty International a Najeriya, ya ce “ni a gani na wannan ba wani sabon abu bane domin kuwa, ita ma gwamnati ko shugaban kasa Muhammau Buhari ya ci gajiyar irin wannan goyon baya a lokacin da yake adawa, kuma anan ganin da goyon bayan kasashen wajen ne ya samu nasara, saboda haka banga dalilin a zai sa gwamnati yanzu ta tada hankalin ta ba.”
Shima wani dan kasa, mai suna Hussaini Mani, cewa ya yi matakin na Amurka abin Allah wadarai ne, kuma baiga dalilin da zai sa Amirka ta rinka saka baki a cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ba, domin ita ma tana da nata matsalar.
A farkon wannan makon ne dai Mista Festus Kiyama da ke zama kakakin yakin neman sake zaben shugaba Buhari ya zargi Jakadan Amurka da marawa Atiku Abubakar baya, bisa la’akari da bashi izinin shiga kasar ta Amurka bayan shekara da shekaru, a wannan lokaci a ake batun zabe.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Babangida JIbrin.
Your browser doesn’t support HTML5