Shugaban Amurka Barack Obama ya kau da yiwuwar Amurka ta dau matakin soji don dakile tashin hankalin da ke samun goyon bayan Rasha a Ukraine, to amma ya ce Amurka da kawayenta na Turai za su dage wajen ganin an shawo kan tashin hankalin.
Da ya ke jawabi jiya Alhamis, saura kiris Mr. Obama ya ce matakin sojin da Rasha ta dauka a Ukraine mamaya ce. Ya ce Rasha ta yi makwanni ta na keta diyaucin kasar Ukraine da gangan kuma akai-akai, sannan ya yi gargadin cewa da yiwuwar Rasha ta sake fuskantar takunkumin tattalin arziki daga kasashen Yamma. Shugaba Obama ya kuma ce ya tattauna da Shugabar Jamus Angela Merkel kan halin da ake ciki a Ukraine. Daga bisani Fadar Shugaban Amurka ta White House ta fitar da wata takardar bayani mai cewa Shugabannin biyu sun jaddada kudurinsu na hada kai don samo mafita a diflomasiyyance.
Shugaban ya yi magana da manema labarai 'yan sa'o'i bayan da takwaransa na Ukraine Petro Poroshenko ya ce sojojin Rasha tafe da tarin makamai sun ketaro zuwa gabashin Ukraine inda su ka kwace garin Novoazovsk mai tashar jirgin ruwa.