Hukumomin Amurka sun kama wani dan Najeriya Daniel Adekunle Ojo, kan zargin zamba ta internet.
'Yansanda a jahar Carolina ta Arewa, sun kama Mr.Ojo ne saboda irin rawar da ya taka wajen satar bayanan haraji na mutane 1,600, ma'aikatan hukumar ilmi a wata gunduma da ake kira Glastonbury dake jahar Connecticut.
Masu gabatar da kara suka ce Ojo, yayi amfani da wadannan bayanan ya shigar da takrdun haraji na mutane 122.
Har ma tuni hukumar karbar haraji ta Amurka ta biya dala dubu 37,000 zuwa asusun ajiyar bankuna daban daban, watau kimanin Naira milyan 13 ke nan.
Haka nan masu gabatar da karar suka ce sun yi a mannar cewa, Ojo yana da hanu a wasu satar bayanan da aka yiwa irin wadannan ma'aikata a wasu gundumomi biyu, daya a jahar Connecticut, guda kuma a jahar Minnestota.
Wani Alkali ya bada umarnin a tsare shi a jahar Carolina ta arewan, daga nan a tusa keyarsa zuwa Connecticut.
Jami'ai suka ce Ojo ya shigo Amurka ne a bara da visar masu kawo ziyara, amma yaki barin kasar bayan da wa'adin zamansa ya kare a wata shidan bara.