Amurka ta kama ta kuma tuhumi wani tsohon babban jami'in kamfanin kera motoci ta Volkswagen a Amurka kan zargin hada baki da niyyar zambar Amurka kan magudin irin hayaki da motocin kamfanin suke fitarwa.
WASHINGTON DC —
Jami'in mai suna Oliver Schmidt, wanda tsohoin janar manaja ne a sashen fasaha da muhalli na kamfanin a Amurka, ya bayyana na wani dan gajeren lokaci jiya Litinin a wata kotun Amurka a Miami, bayan da aka kama shi ranar Asabar a Florida. Bai gabatar da amsa kan zargin da aka yi masa ba.
Schmidt, shine mutum na biyu da aka kama dangane da binciken da gwamnatin Amurka take yi kan kamfanin na Volkswagen, zargin da kamfanin ya amsa cewa ya makala wasu na'urori kan akalla motoci milyan 11 da aka sayar a fadin duniya, wadda zai iya boye irin hayaki da motocin suke fitarwa, matakin da hukumomi suka ce ya saba dokar kare muhalli da iska ta Amurka.