Amurka Ta Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabon Takunkumi

Shugaban Amurka Barack Obama a hagu, shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a Dama

Amurka ta kakabawa Koriya ta arewa sababbin takunkumi a maida martani kan kutsen da tayiwa kamfanin fina finai na Sony bara.

Amurka ta kakabawa Koriya ta arewa sababbin takunkumi a maida martani kan kutsen da tayiwa kamfanin fina finai na Sony bara.

Shugaban Amurka Barack Obama ya sa hannu a wani umarnin shugaban kasa jiya jumma’a na bada izinin takunkumin.

Fadar White House tace takunkumin zai shafi wadansu cibiyoyi uku da mutane goma, a matsayin matakin farko na ladabtar da Koriya ta arewa sabili da takalar da take yi da ya hada da kai hari kan hanyoyin sadarwar internet.

Ma’aikatar kudin Amurka tace sababbin takunkumin zasu kara tsananta wadanda aka riga aka kakabawa Koriya ta arewa ta wajen hana wadansu mutane hulda da cibiyoyin kasuwancin Amurka da kuma hana Amurkawa hulda da Koriya ta Arewa.

Koriya ta arewa ce tafi kowacce kasa yawan takunkumi a duniya, sabili da haka takunkumin da aka kakaba mata jiya jumma’a mai yuwuwa ne ya zama na jeka na yika kawai.