Amurka Ta Hallaka 'Yan al-Shabab 35

  • Ibrahim Garba

Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Farmajo

A cigaba da hare-haren da Amurka ke kai wa kan mayakan kungiyoyi masu tsaurin ra'ayi a Afirka, ta kashe mayakan al-Shabab a kalla 35 a hari na baya bayan nan.

Hare-haren jiragen Amurka sun hallaka ‘yan ta’addan al-Shabab 35 a yankin tsakiyar Somaliya, a cewar hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon jiya Litini.

Ranar Lahadi ne aka kai wannan harin a yankin Hiran, a yayin da mayakan ke ta kaura daga nan zuwa can a yankunan karkara … saboda su kara yawan mayakansu,” bisa ga wani bayani na bataliyar rundunar sojojin Amurka da ke aiki a Afirka.

Amurka ta zafafa hare-haren jiragen sama kan ‘yan al-Shabab tun daga farkon wannan shekarar. Kungiyar mayakan na so ne ta kafa kasa mai tsattsauran ra’ayin addini a Somaliya.

Mayakan kungiyar Tarayyar Afirka sun fatattaki mayakan al-Shabab daga Mogadishu babban birnin kasar. To amma har yanzu masu tattsauran ra’ayin kan kai hare-hare a cikin birnin, kuma su na rike da wurare da dama a yankin tsakiyar kudancin Somaliyar.