Amurka da kawayenta na Turai sun ce mummunan sabon fadan nan da ya barke a Sudan Ta Kudu ya saba ma yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma a kasar, kuma su na kiran da a gaggauta kawo karshen fadan.
A wata takardar bayani ta hadin gwiwa da Amurka da Burtaniya da Norway, da ake kira Troika, su ka fitar jiya Laraba, sun ce fadan da ake yi a wajejen garin Yei wani mummunan karan tsaye ne ga yarjejjeniyar kwance damara da aka cimma a watan Disamba na 2017 da kuma yarjajjeniyar da aka farfado da ita wadda gwamnatin Sudan Ta Kudu da kuma kungiyoyin ‘yan tawaye da dama su ka cimma a watan Satumban da ya gabata.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ba da rahoto a makon jiya cewa fada tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun ‘yan tawaye y a raba mutane wajen 13,000 da muhallansu ta yadda wajen 5,000 su ka tsere zuwa Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo (Congo).