Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce sabbin matakan da aka dauka na mayar da martani ne kan shigen irin matakan da China ta dauka don jami'an diflomasiyyar Amurka da ke China.
WASHINGTON, D.C. —
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da wasu sabbin matakai akan jami’an diflomasiyyar kasar China da ke aiki a Amurka.
A karkashin sabbin matakan, da sakatare Mike Pompeo ya sanar a jiya Laraba, dole ne manyan jami’an diflomasiyyar China su nemi izini daga hukumomin kasar kafin su kai ziyara wata kwaleji a kasar ko kuma su gana da jami’an kananan hukumomi, haka kuma idan za su yi wani taron al’adunsu a wajen ofishin jakadancin China ko kananan ofisoshin jakadancin Chinar idan mahalarta taron sun wuce 50.
Pompeo ya kara da cewar gwamnatin Amurka zata bukaci gwamnatin China ta bayyana duk wasu shafukan sada zumunci na yanar gizo da ke karkashinta.