Amurka Ta Fara Neman Rigakafin Coronavirus

Wata likita yayin da ta ke gwajin wasu kwayoyi.

Dakarun Amurka na taimaka wa wajen neman rigakafin cutar Coronavirus da ke saurin kisa, yayin da likitoci ke da sauran watanni 12 zuwa 18 a yunkurin da suke yi na ganin sun  samar da rigakafin cutar ga jama’a.

Likitoci daga cibiyoyin bincike na soji da ke Fort Detrick da Walter Reed sun fada wa manema labarai a ma’aikatar tsaro ta Pentagon cewa, a jiya Alhamis tawagoginsu sun gano wata allurar rigakafi “da ke nuna alamun” za ta yi aiki.

A cewarsu ba za a iya rubayanta ba, ta yadda Cibiyar Lafiya ta kasa za ta iya aiki akanta.

Dr. Kayvon Modjarrad, Darekta a cibiyar bincike ta Walter Reed, ya ce sojojin Amurka na gwada sinadaran rigakafin cutar ta Coronavirus akan kananan beraye.

Daga baya kuma za a gwada ta ne kan manyan dabbobi domin a tabbatar da cewa ba za ta yi illa ga bil Adama ba.

Hakan na faruwa ne yayin da aka bayyana mutum na goma da ya mutu sanadiyyar cutar a jihar Washington a nan Amurka.

Lamarin da Jeff Duchin, jami’in lafiya a jihar ta Washington ya ce, na cike da sarkakiya.