Fadar Shugaban Amurka ta White House ta bayyana matukar damuwarta a jiya Lahadi, kan rahotannin da ke nuna cewa sojoji na ta kwarara zuwa gabashin Ukraine daga Rasha mai makwabtaka da wurin, ciki har da ketara kan iyakar da ake yi da manyan makamai da tankokin yaki.
Mai magana da yawun Kwamitin Tsaro na Kasa Bernadette Meehan, ita ma ta yi gargadin cewa
duk wani take-taken 'yan tawaye masu ra'ayin Rasha na kwace karin yankuna a gabashin kasar mai fama da rigingimu, za’a dauke shi a matsayin saba ma yarjajjeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin 'yan tawayen da gwamnatin Ukraine.
Wannan gargadin Amurkan na baya-bayan nan, ya zo ne a daidai lokacin da masu sa ido na Turai su ka ba da rahoton ganin tawagar manyan makamai na tafiya gabashin Ukraine, a yayin da ake mummunan barin wuta a birnin Donetsk da ke karkashin ikon 'yan tawaye.
Meehan ta yi kira ga bangarorin biyu da su yi cikakken mutunta yarjajjeniyar da aka cimma a watan Satumba, musamman ma alkawarin Rasha na kawo karshen ketara kan iyakarta da ake yi da sojoji da makamai.